’Yan sanda sun cafke riƙaƙƙun masu fashin ƴan “one chance” su uku da ake alaƙanta su da kisan lauya a Abuja

police 750x430

Rundunar ’yan sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta sanar da cafke wasu shahararrun mutane uku da ake zargi da hannu a kisan wata lauya mazauniyar Abuja mai suna Nwamaka Chigbo.

Chigbo, wadda tsohuwar ma’ajin kungiyar Lauyoyi ta ƙasa reshen Babban Birnin Tarayya Abuja,  wadda lamarin ya faru a kan ta tana gefen hanya yayin da wata ƙungiyar masu laifi ta “one chance” ta kai mata da misalin ƙarfe 5:50 na yammacin ranar 5 ga Janairu, jim kaɗan bayan ta shiga wata baƙar mota kirar Volkswagen Golf 3 a titin Kubwa.

A dai wannan ranar an gano wata mai jinya a Asibitin Kiwon Lafiya na Tarayya Jabi mai suna Chinemerem Chuwumeziem wadda ita ma ake zargin ’yan “one chance” ne suka kashe ta.

Bayan waɗannan abubuwa, Kungiyar Lauyoyin Najeriya ta bukaci Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, da ya ɗauki dawowar laifukan “one chance” a Abuja a matsayin gaggawar tsaro.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Babban Birnin Tarayya, Josephine Adeh, ta fitar, ta bayyana cewa mutanen da aka cafke ’yan wata ƙungiyar fashi sa makami ta “one chance” ne, kuma cafkewar ta biyo bayan umarnin Kwamishinan ’yan sanda na Babban Birnin Tarayya, Miller Dantawaye, na ganin an gurfanar da duk masu hannu a kisan.

Adeh ta ƙara da cewa an cafke mutanen tsakanin Juma’a da Asabar a yankunan Dei-Dei, Dakwa da Dan-Tata a Kubwa, bayan bin sawun wayar salular mamaciyar ta hanyar dabarun binciken sadarwa, inda binciken farko ya nuna sun shafe shekaru suna aikata laifuka a Babban Birnin Tarayya, musamman a lokutan bukukuwa.

Ta bayyana sunayen waɗanda aka cafke da Saifullahi Yusuf mai shekara 22, Ishau Yusuf mai shekara 24, da Minka’ilu Jibril wanda aka fi sani da Dan-Hajia, dukkansu ’yan jihar Kaduna, inda ta ce Saifullahi da Ishau ’yan’uwa ne, kuma sun amsa laifin kai hari, ƙoƙarin karɓar kuɗin fansa, da satar wayar Android ɗin mamaciyar wadda suka sayar a Dei-Dei kan naira 120,000, yayin da ake ci gaba da bincike domin cafke wani da ya tsere da gano sauran mambobin ƙungiyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here