‘Yan Bindiga sun sake kai wani sabon hari Jihar Plateau

'Yan bindiga, Kujuru, mata, sace, hari
‘Yan bindiga sun sake kai wani sabon hari garin Banono da ke karkashin masarautar Kufana ta karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna a tarayyar Najeriya,..

Kimanin mutane 30 ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kauyen Kwahaslalek da ke karamar hukumar Mangua ta jihar Filato a safiyar ranar Laraba.

An bayyana cewa wadanda harin ya rutsa da su yawancinsu mata ne da kananan yara, sun garzaya gidan wani shugaban al’umma da ke yankin ne a daren ranar Talata domin tsira da rayukansu sakamakon rikicin da ya barke da rana a garin Mangu inda ‘yan bindigar suka kewaye su tare da kashe su baki daya.

Karanta wannan: Kotu ta tasa keyar Danbilki Kwamanda zuwa Gidan Yari

Wani shugaba a yankin, Mark Haruna ya tabbatar da adadin wadanda suka mutu a Jos, babban birnin jihar a ranar Laraba.

Haruna ya ce, “Abin da ya faru a Sabon Gari da garin Mangu a jiya da rana, abin ya dame shi ne kawai don a kawar da hankalin jama’a daga kauyuka.

Karanta wannan: Badakalar Naira Biliyan 4: Tsohon Gwamnan Anambra Obiano ya isa Kotu

“A karo na biyu, kauyena Kwahaslalek a bayan sansanin NYSC, ya fuskanci hari da wasu ‘yan bindiga a jiya Talata. Sun zo ne da misalin karfe 12:30 na safe, suka kashe sama da mutane 25, galibi mata da kananan yara ne.”

Shugaban kungiyar ci gaban Mwaghavul, Joseph Gwankat shi ma ya tabbatar da kisan yana mai bayyana shi a matsayin rashin tausayi.

“Ban iya yin bacci a daren jiya ba sakamakon abin da ya faru jiya a garin Mangu da rana, yanzu dai an shaida min cewa an kai hari kauyen Kwahaslalek a daren jiya kuma an kashe mutane kusan 30″.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here