’Yan Bindiga Sun Sace Iyalan Dagaci A Taraba

Nigeria Kidnappings Bandits deputy
Nigeria Kidnappings Bandits deputy

’Yan bindiga sun sace mata biyu da ’ya’ya shida na Dagacin Mutumbiyu a Jihar Taraba.

Bayanan da Aminiya ta kalato sun nuna ’yan bindigar sun kai hari gidan basaraken ne da ke Jalingo, babban birnin jihar, da tsakar dare a ranar Alhamis inda suka kwashi ahalin nasa.

Basaraken, Mai Shari’a Sani Muhammed (mai murabus), ba ya gidan nasa a lokacin da maharan suka kai farmakin.

Majiyarmu ta ce, maharan sun kira basaraken a kan ya same su don tattauna yadda za a saki iyalan nasa.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan jihar, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

“An sace mata biyu da ’ya’ya shida na Dagacin Mutumbiyu da misalin karfe 1:00 na dare ranar Alhamis, kuma ana kokarin yadda za a kubutar da su,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here