‘Yan bindiga sun kone matafiya har lahira a Sokoto

Bandits
Bandits

‘Yan bindiga sun kone akalla matafiya arba’in da biyu har lahira a karamar hukumar Sabon Birni dake jihar Sokoto.

Rahotanni sun bayyana cewa matafiyan da aka kona suna kan hanyar su ta yin kaura zuwa wasu sassan kasar nan saboda matsalar tsaro da yankin nasu yake fuskanta.

Shaidun gani da ido sun shaidawa BBC cewa lamarin ya faru ne a ranar litinin din data gabata da misalin karfe tara na dare.

Wani magidanci ya shaidawa manema labarai cewa cikin mutanen da lamarin ya rutsa dasu akwai matar sa da ‘ya’yan sa guda hudu da kuma dan uwan mahaifiyar sa. Inda ya bayyana cewa a lokacin da suka isa wajen da lamarin ya faru sun kirga gawarwakin mutane akalla ashirin da biyar.

Ya kara da cewa kadan daga cikin mutanen da al’amarin ya rutsa dasu ne suka tsira, inda ya bayyana cewa mutane arba’in da biyar ne a motar, amma mutane bakwai ne suka tsira wanda yanzu haka suna asibiti suna karbar magani.

Zuwa yanzu dai rundunar ‘yan sanda bat ace komai kan wannan lamari ba.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here