Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta ce ta kama kwantenoni 21 na kayayyakin magunguna marasa rajista tare da kwayar tramadol a tashar jiragen ruwan Apapa da ke Legas a shekarar 2018.
Darakta-Janar ta hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana hakan ranar Litinin a Abuja a wani taron manema labarai domin nuna nasarorin da hukumar ta samu a fannin sarrafa abinci da magunguna.
Ta ce nasarar da aka samu ta biyo bayan rahoton sirri da fadar shugaban kasa ta fitar na cewa wasu marasa kishin kasa na shirin shigo da gurbatattun kaya da ba su da rijista zuwa Najeriya daga kasar Indiya.
Ta ce hukumar ta NAFDAC ta hada gwiwa da hukumar kwastam ta kasa inda daga karshe aka sauke kwantena 21 a tashar jirgin ruwa ta Apapa da ke Legas.
Adeyeye ta bayyana cewa, dukkan kwantenonin an nuna cewa kayan gini ne a cikin su, amma a lokacin da aka duba abubuwan da ke cikin, an gano wasu kwantena biyu ne kawai dauke da kayan gini.
A cewar Adeyeye, an karkatar da guda hudu daga cikin kwantenan zuwa tashar ruwan Tema da ke Ghana, amma daga baya aka dawo da su Cotonou, bayan da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Ghana ta samu bayanan hukumar NAFDAC.
Ta bayyana cewa hukumar NAFDAC ta hada kai da jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin tare da tabbatar da cewa an kama guda biyar daga cikin kwantenan da suka shigo tashar ruwan kasar bisa bukatar hukumar NAFDAC.
Shugabar NAFDAC ta ce hukumar ta kuma samu rahoton cewa an lalata wadannan kwantenoni a Jamhuriyar Benin.
A cewarta, a karshe dai gwamnatin Jamhuriyar Benin ta amince ta hada hannu da takwararta ta Najeriya domin aiwatar da lalata kwantenonin a Cotonou.
Ta ce, kayayyakin da ba a yi wa rajistar ba, tare da tramadol masu nauyin milligrams daban-daban a cikin manyan kwalaye, an lalata su ne a watan Disambar 2022, kuma kayayyakin sun kai Naira biliyan 95.













































