Ya kamata a dage babban taron APC zuwa wani lokaci- ‘ya’yan APC na Burtaniya

7E1BC223 1269 4741 82B3 D80EADE98F6C
7E1BC223 1269 4741 82B3 D80EADE98F6C

A yayin da jam’iyyar APC mai mulki ke shirin gudanar da babban taronta na kasa, ‘ya’yqn jam’iyyar dake zaune a kasar Birtaniya sun shawarci kwamitin riko nq jam’iyyar da ya ci gaba da aiki, maimakon Maimakon shirya zabe, kamata jam’iyyar ta karfafa kan nasarorin da kwamitin riko ya samu karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni.

Jam’iyyar APC ta shirya gudanar da babban taronta na kasa a ranar 26 ga Fabrairu, 2022, bayan kokarin da ake yi na hada kan bangarori daban-daban a fadin jihar.

Sai dai Dr. Philip Idaevor, shugaban jam’iyyar APC a kasar Birtaniya, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Talata, ya bukaci hukumar zaben ta sauya babban taron kasa zuwa wani lokaci.

Ya bukaci kwamitin zartaswa na jam’iyyar APC na kasa da ya gaggauta dage babban taron kasa daga ranar Asabar 26 ga watan Fabrairu domin a warware wasu muhimman batutuwa, musamman a yanzu da kwamitin sulhu karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu ya bukaci karin mako guda domin kammala aikinsa.

A cewar sanarwar, shawarar za ta tabbatar da samun halartar ‘ya’yan jam’iyyar na kasashen ketare.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here