Wata ƙungiya ta nuna goyon baya ga Ministar Mata a shirin sabunta Fata

WhatsApp Image 2025 09 16 at 22.03.50 750x430

Ƙungiyar tabbatar da gaskiya da adalci ga jama’a ta (Social Integrity Network – SINET) ta bayyana gamsuwa da jajircewa da kuma nasarorin da Ministar Mata, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta cimma tun bayan karɓar ragamar ma’aikatar a watan Oktoba, shekara ta 2024.

Ƙungiyar ta ce ministar ta taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da shirin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na sabunta fata (Renewed Hope Agenda).

A cewar shugabannin ƙungiyar bayan taro da suka gudanar a birnin Abuja, ministar ta tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban mata a faɗin ƙasar.

Haka kuma ta jajirce wajen tabbatar da adalci, nagartaccen aiki da kuma ƙarfafa haɗin kai a tsakanin mata, lamarin da ya tabbatar da jajircewarta ga al’umma.

Shugaban ƙasa na ƙungiyar, Dalhatu Issah, ya bayyana cewa ministar ta nuna ƙwarewa da ƙwazo wajen sauke nauyin da aka dora mata.

Ya ce ayyukanta sun tabbatar da basirarta a matsayin mai kare martabar mata da kuma jajirtacciyar ‘yar ƙasa wadda ke aiki ba tare da son zuciya ba.

Rahoton ya nuna cewa tun daga hawanta kan mukamin, an samu sababbin shirye-shirye masu amfani da suka haɗa da taron tattaunawa da tsofaffin ministocin mata, wakiltar Najeriya a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan Matsayin Mata karo na 69 a birnin New York, da shirya taron tattaunawa na ƙasa a ranar 29 ga watan Mayu, shekara ta 2025.

Haka kuma ta gudanar da taro na musamman domin cika kwanaki 100 a ofis, inda aka raba tallafi da tsarin wutar lantarki ta hasken rana ga ƙungiyoyin mata.

Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa ma’aikatar ta cimma gagarumar nasara wajen ƙarfafa tattalin arziƙin mata ta hanyar shirye-shiryen bunƙasa sana’o’i.

A cewarta, an tallafa wa mata sama da 30,000 a jihohi 18 da Abuja ta hanyar rabon kayan tallafi da shirye-shiryen dogaro da kai. Haka kuma an kafa cibiyar sarrafa shinkafa a Jihar Neja wadda ta amfanar da mata sama da 1,500.

Baya ga haka, an haɗa kai da hukumar tsaron farin kaya domin koyar da matan sojoji da suka rasu a sana’o’in dogaro da kai, tare da haɗin gwiwar wani banki na cikin gida domin horas da mata sama da 500 a fannoni daban-daban irin su dinki, girki da gyaran gashi.

Haka kuma ministar ta tallafa wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, wanda ya taimaka wajen samun nasarar lashe kofin gasar ƙasashen Afirka ta mata karo na 13 a Morocco.

Daga ƙarshe, ƙungiyar ta gode wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa zabar minista mai kishin ƙasa da kula da muradun jama’a.

Ta kuma bayyana cikakkiyar amincewarta da ayyukan Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim, tare da kira ga ‘yan Najeriya da su mara mata baya domin ci gaba da tafiyar da ingantattun shirye-shiryen da ta ke jagoranta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here