An buɗe sansanin tawagar Super Eagles ya a hukumance a ranar Lahadi a birnin Rabat na ƙasar Morocco, inda ‘yan wasa goma na farko suka isa domin fara shirin karshe na wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA na 2026.
Rukunin farko na ‘yan wasa da jami’an tawagar sun isa otal ɗin Rive da ke Rabat a yammacin Lahadi, wanda ke nuna fara mako mai muhimmanci a ƙoƙarin Najeriya na komawa matakin gasar ƙwallon ƙafa mafi girma a duniya.
Jami’in hulɗa da jama’a na tawagar, Promise Efoghe, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN cewa cikin waɗanda suka isa farko akwai Calvin Bassey, Alex Iwobi, Samuel Chukwueze, Tolu Arokodare da Olakunle Olusegun.
Daga bisani a ranar Lahadi, Wilfred Ndidi, Moses Simon da William Troost-Ekong suka bi sahu, wanda ya kai yawan ‘yan wasa takwas.
Daga baya kuma Benjamin Fredericks da Chidozie Awaziem suka isa, wanda ya cika adadin ‘yan wasa goma da ke cikin sansanin yayin da horon ya fara ƙaruwa.
Rahotanni sun ce, kocin tawagar, Eric Chelle, ya kammala jerin ‘yan wasa 24 da zai yi amfani da su a wasan neman gurbi, inda ya haɗa fitattun ‘yan wasa daga Turai da na gida don tunkarar muhimman wasanni a Rabat.
Super Eagles za ta fara fafatawa da Gabon a ranar Alhamis, inda nasara za ta ba su damar shiga wasan karshe da za su fafata da Kamaru ko Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo a ranar 16 ga watan Nuwamba, a babban birnin Morocco.
Wasannin neman gurbi na ƙasashen Afirka na wannan zagaye suna ba ƙasashe damar ƙarin hanya zuwa gasar cin kofin duniya ta 2026, sai dai duk wanda ya yi nasara daga wannan zagaye zai sake buga wasan neman gurbi da ƙungiyar daga wata ƙasa a sauran nahiyoyi a watan Maris 2026 a ƙasar Mexico.
Tawagar da Chelle ya zaɓa ta samu sauye-sauye daga wadda ta taka leda a watan da ya gabata, inda Najeriya ta samu nasarori a kan Lesotho da Benin, wanda hakan ya basu damar shiga wasan neman gurbi a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da suka zo na biyu mafi kyau a cikin rukuni tara na Afirka.
Daga cikin waɗanda suka dawo cikin tawagar akwai Maduka Okoye daga ƙungiyar Udinese don ƙara ƙarfin gasa a raga, tare da Awaziem da ya dawo daga tsaro. Haka kuma Raphael Onyedika da Chidera Ejuke sun dawo don ƙara ƙwarewa a tsakiyar fili da gaban gaba.
An cire Felix Agu, Terem Moffi da Christantus Uche daga jerin wannan karon.
Najeriya ce ƙasar da ta fi sauran ƙasashe hudu na wannan zagaye samun matsayi a jerin ƙasashen FIFA, inda ake ganin tana da damar kaiwa gaba, sai dai kocin ya yi gargaɗi da cewa dole ne su guji sakaci tare da mayar da hankali kan dabaru da tsari.












































