Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya sake naɗa Dakta Ahmed Abubakar Audi a matsayin Babban Kwamandan Hukumar Tsaro ta (NSCDC) na wa’adin shekaru biyar.
Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, inda ya ce sabom naɗin ya fara aiki daga ranar Juma’a, 27 ga Fabrairu, 2026.
An fara naɗa Dakta Audi a wannan muƙami ne a shekarar 2021 ta hannun tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Wa’adinsa na farko na shekaru biyar ya ƙare a ranar Juma’ar da ta gabata, yayin da ya halarci bukukuwan Ranar Tsaro ta Duniya ta 2026 a Hedikwatar NSCDC da ke Abuja.
Sanarwar ta ce zai koma bakin aikinsa a ranar Litinin, 2 ga Maris, tare da sabon umarni.
Onanuga ya ce Shugaba Tinubu ya umarci Audi da ya sake fasalin hukumar domin ta taka muhimmiyar rawa a fannin tsaron ƙasa, musamman yayin da rundunar ‘yan sanda ke mayar da hankali kan babbar aikinta na kare ‘yan ƙasa daga ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda.
An haifi Dakta Audi a ranar 30 ga Satumba, 1967, a garin Laminga da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa, Jihar Nasarawa.
Bayan kammala karatunsa na firamare da sakandare a jihar, ya halarci Kwalejin Horar da Malamai ta Jengre a Jihar Filato, inda ya samu takardar shaidar Teachers’ Grade II a 1987.
Daga bisani ya yi karatu a Kwalejin Ilimi ta Akwanga, inda ya samu takardar NCE a 1992.
Ya ci gaba da neman ilimi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya kammala digiri na farko a fannin Ilimin Jiki da Lafiya a 1995.
A shekarar 2001, ya samu digiri na biyu a fannin Gudanar da Harkokin Mulki daga Jami’ar Calabar.
A 2014, ya samu digirin digirgir (PhD) a fannin Gudanar da Harkokin Mulki daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, sannan a 2019 ya samu digiri na biyu a fannin tsara doka da Shari’ar laifuka “law Enforcement and Criminal Justice” daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.
Dakta Audi ya shiga NSCDC a watan Nuwamba 1996 a matsayin sa-kai, kuma bayan kammala horon jami’i a 1997, aka tura shi a matsayin shugaban sashi a Ƙaramar Hukumar Obi ta Jihar Nasarawa.
Ya yi aiki a rundunonin jihohi daban-daban, kuma a 2007 aka ƙara masa girma zuwa muƙamin Commandant, sannan aka tura shi ofishin Babban Kwamandan Hukumar a Hedikwatar Ƙasa da ke Abuja.












































