TETFund Ta Amince da N130m Ga Makarantun Fasaha.

Asusun Tallafawa Ilimin Manyan Makarantu (TETFund) ya amince da Naira miliyan 130 a matsayin kason shiyya-shiyya ga kowace kwalejin fasaha a cikin shekarar 2023 don inganta ilimin kimiyyar kere-kere a fadin kasar nan.

Daraktan samar da ababen more rayuwa na Asusun, Buhari Mika’ilu ne ya sanar da haka a wani taron wayar da kan jama’a game fashin bakin ababen da kwalejin fasaha ta Amfana a Abuja.

Mika’ilu ya ce sun dauki wannan matakin ne domin karfafa kokarin hukumar kula da fasahar kere-kere ta kasa (NBTE) wajen kara wa makarantun fasaha damar gudanar da aikinsu.

“Saboda haka ne asusun ya ba da fifikon rabon shiyyar na shekarar 2023 ga masanan kimiyyar kere-kere don a samar da su don inganta ilimin kimiyyar kere-kere a fadin kasar nan.

Ya kuma bayyana cewa tun daga lokacin da aka fara shirin shiyya shiyya a shekarar 2016, asusun ya ware jimillar kudi N52,046,079,584.7 ga kwararrun masana kimiyyar kere-kere

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here