Shugaban mulkin sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan ya ce ƙasar za ta amince da tayin da ƙungiyar tarayyar Afrika, AU ta yi na kawo ƙarshen rikici a ƙasar idan an mayar da ita cikin ƙungiyar.
Ƙungiyar ta AU ta dakatar da Sudan ɗin ne bayan da sojoji suka karɓe mulki a watan Oktobar 2021.
Karin labari: An tsare kanal ɗin soji a Mali bayan wallafa littafi
A ranar Lahadi ne janar Burhan ya gana da tawagar da ƙungiyar AU ta kafa domin kawo ƙarshen rikin da ke faruwa a ƙasar, wadda Mohamed Ibn Chambas ke jagoranta.
Tawagar mai mambobi uku zata shiga tsakanin wajen tattaunawa da maido da ƙasar kan turbar dimokradiyya, inda zata yi aiki da masu ruwa da tsaki ‘ƴan Sudan na cikin gida da waje domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Karin labari: Hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutum 12 da jikkatar mutum 28
A wata sanarwa da janar Burhan ya wallafa a shafinsa na Facebook ya bayyana ƙwarin guiwa kan ƙungiyar ta AU da yiwuwar kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a ƙasar, amma ya nemi a mayar da Sudan cikin AU ta zama cikakkiyar mamba.