Majalisar dattawan Najeriya, ta karɓi ƙudirin dokar halasta kuɗaɗen haram da kuma dokar yaƙi da ta’addanci wadda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya aike mata domin tantancewa tare da sahale aiki da su.
Ƙudirin dai na tare da wasiƙar da shugaban majalisar dattawan Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisar yau Alhamis.
A cikin wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan 12 ga wannan wata da muke ciki na Afrilu, shugaba Buhari ya ce, bukatar amincewa da ƙudirorin biyu ya ta samo asali ne bisa tanadin sashe na 58 (2) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima.
Haka kuma, Ya bayyana cewa gazawar da ke cikin dokar Anti-Money Laundering/Combating the Financing of Terrorism regime (AML/CFT), ya sa ya zama wajibi a zartar da kudirorin biyu.
Shugaban ya ƙara da cewa, rashin amincewa da ƙudurorin biyu ka iya haifar da hatsarin da zai iya haifar da sanya Najeriya cikin jerin sunayen da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya FATF ta yi.
Buhari a cikin wasikar ya ce: “Bisa ga sashe na 58 (2) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), na gabatar da wannan ƙudirin dokoki ta dokar halasta kudaden haram ta 2022 da kuma dokar yaƙi da ta’addanci ta 2022.
“Bayan tantancewar, Ma’aikatar Shari’a da sauran masu ruwa da tsaki sun yi nazari kan gazawar da aka yi kuma suka tsara dokokin.
“Wannan zai haifar da wasu munanan sakamako ga tattalin arzikinmu mai saurin bunkasuwa.













































