Mataimakin bulaliyar majalisar Dattawa kuma Sanata daga Kano ta Tsakiya Sanata Rufai Hanga ya bayyana rashin goyon bayansa ga shirin kafa ’yan sandan jihohi, yana mai cewa wannan tsarin zai iya zama makamin siyasa a hannun gwamnonin jihohi wajen danniya da tsoratar da masu adawa.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa, Sanata Hanga ya yi wannan jawabi yayin zantawar sa da manema labarai a Kano.
Hanga ya ce kafa ’yan sandan jihohi zai haifar da sabuwar takaddama tsakanin jami’an tsaron tarayya da na jihohi sakamakon rikicewar muradun manyan ’yan siyasa da ake kira “Siyasar Ubangida”.
Ya bayyana cewa wannan rikici zai ƙara ta’azzara matsalolin tsaro da ’yan ƙasa ke fuskanta, tare da barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin ƙasar.
Hanga ya ce shirin kafa rundunar tsaro ta jihohi zai buɗe sabon babi na cin zarafin siyasa, inda za a iya amfani da jami’an tsaro wajen murƙushe masu sukar gwamnati ko kuma ɓata muradun masu adawa.
Sanatan ya kuma bayyana damuwarsa kan matakin janye jami’an tsaro daga manyan mutane, yana mai cewa hakan na iya barin wakilan jama’a cikin haɗari, musamman ganin yadda matsalolin tsaro ke ƙaruwa a sassan ƙasar nan.
Ya yi kira ga ’yan majalisa da su yi watsi da shirin, tare da mai da hankali kan gyarawa da ƙarfafa rundunar ’yan sandan tarayya domin tabbatar da adalci da bin doka ba tare da son rai ba.
Sanatan ya kuma bayyana cewa ya ɗauki nauyin ƙudurin kafa Jami’ar Noma a Kura, wadda ta riga ta wuce karatu na farko da na biyu a majalisa, tana jiran karatu na uku da kuma amincewar shugaban ƙasa.
Hanga ya nanata cewa wajibi ne ’yan Najeriya su haɗa kai wajen kare dimokuraɗiyyar ƙasar, tare da nisantar duk wani tsari da zai iya raunana mulkin doka da haifar da zaluncin siyasa.













































