Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta roki Shugaba Tinubu ya shiga tsakanin rikicin masarautar Kano

Tinubu, Sanusi, Gwamnatin, roki, Shugaba, shiga, tsakanin rikicin, masarautar, Kano
Gwamnatin jihar Kano ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya sa baki a rikicin da ke faruwa a masarautar Kano.Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Gwarzo,..

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Gwamnatin jihar Kano ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya sa baki a rikicin da ke faruwa a masarautar Kano.

Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ne ya yi wannan kiran yayin ganawa da manema labarai a gidan gwamnati ranar Litinin.

Ya ce shiga tsakani na Tinubu zai ceto jihar daga fadawa cikin rudani.

Karin labari: Da Dumi-Dumi: Gwamnatin tarayya ta dakatar da aikin jirgin saman Najeriya na wani lokaci

Gwarzo ya ce jihar ta yi suna wajen zaman lafiya da kwanciyar hankali, duk da sarkakiyar siyasa da ta ke da su.

Mataimakin gwamnan ya bukaci shugaban kasar da ya dauki matakan da suka dace don hana faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta bi tsarin da ya dace wajen mayar da Sarki Sanusi Lamido Sanusi kan kujerarsa ta saurauta.

Karin labari: Hajjin Bana: Gwamna Yusuf ya kaddamar da jirgin farko na Alhazan Kano

Gwamnati ta amince da sauye-sauyen da aka yi wa dokar Masarautar Kano da kuma kalubalen da ke ci gaba da fuskanta.

Gwarzo ya bayyana cewa ba a baiwa gwamnatin jihar da wani umarnin kotu dangane da lamarin ba.

Mataimakin gwamnan ya ce rokon nasa na da nufin tabbatar da warware takaddamar cikin lumana da kuma tabbatar da zaman lafiyar jihar kamar yadda NAN ta rawaito.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here