Peter Obi Ya Fadi Gaskiyar Abinda Ya Faru Kan Zargin Kulle El-Rufa’i a Anambra 

Screenshot 20221018 061530
Screenshot 20221018 061530

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyar LP, Peter Obi, ya musanta zargin cewa ya kama tare da garkame gwamna El-Rufai na jihar Kaduna a Anambra lokacin yana matsayin gwamna.

Jaridar Vanguard ta ruwaito Obi na cewa babu dalilin da zai sa ya ba da umarnin da tsare gwamnam domin kwamishinan yan sanda a lokacin ɗan arewa ne.

Yace, “Babu hanya ba zan taba yin haka ba. Ban umarci AIG ya kama ko ya tsare wani ba, lokacin ina da Ɗan sandan da babu irinsa a Najeriya, ɗan asalin Kano ne. Kwamishinam yan sanda a lokacin ɗan Adamawa ne.”

“AIG da aka turo a zaben ɗan jihar Nasarawa ne daga arewa. Ku faɗa mun taya zan amfani da karfi na har na bada umarcin tsare wani, ba ta yadda zan yi haka, ban umarci wani ya yi haka ba a matsayin gwamna.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here