Hukumar kula da hasashen yanayi ta ƙasa (NiMet) ta sanar da cewa za a samu ruwan sama da ƙaƙƙarfar iska a sassa daban-daban na Najeriya daga ranar Juma’a zuwa Lahadi.
A hasashen da ta fitar a Abuja ranar Alhamis, NiMet ta bayyana cewa za a yi ruwan sama mai ɗauke da guguwar iska a wasu sassan jihohin Arewa kamar Kebbi, Sokoto, Zamfara, Kaduna, Kano, Katsina da Taraba a safiyar Juma’a, yayin da sauran jihohi irin su Bauchi, Gombe da Adamawa za su fuskanci irin wannan yanayi daga baya.
Hukumar ta ce a tsakiyar ƙasar za a fara da yanayi mai girgije da hasken rana a safiya, sannan daga baya a sami ruwan sama a Nasarawa, Kwara, Benue, Kogi, Filato da Babban Birnin Tarayya.
A kudancin Najeriya kuwa, ruwan sama mai tsanani zai rika sauka a jihohi da dama ciki har da Lagos, Ogun, Akwa Ibom da Cross River, tare da yiwuwar ambaliyar ruwa.
A ranar Asabar, NiMet ta hango yanayi mai girgije da ruwan sama a Arewa, musamman a jihohin Taraba, Adamawa, Bauchi, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Zamfara, Kano da Katsina.
Labari mai alaƙa: NiMet ta yi hasashen samun ruwan sama da tsawa na tsawon kwanaki 3 a faɗin ƙasar
A Kudu kuma, ruwan sama zai rika sauka a jihohin Edo, Imo, Rivers, Delta, Bayelsa, Cross River da Akwa Ibom.
A Lahadi, hasashen ya nuna cewa Arewa za ta fuskanci guguwar iska tare da ruwan sama a Kano, Katsina, Jigawa da Yobe, yayin da a tsakiyar ƙasar irin wannan yanayi zai shafi Abuja, Nasarawa, Filato da Benue. A kudancin ƙasar kuwa, jihohi irin su Oyo, Ogun, Lagos, Edo, Delta, Rivers da Akwa Ibom za su sami ruwan sama.
NiMet ta shawarci direbobi da su guji tuƙi a lokacin ruwan sama mai yawa, sannan ta gargadi manoma da kada su yi amfani da takin zamani da magungunan kashe kwari kafin ruwan sama.
Haka kuma ta bukaci jama’a da su nisanci bishiyoyi masu tsawo da su cire na’urorin lantarki daga soket domin gujewa haɗurra.
Hukumar ta kuma bukaci kamfanonin jiragen sama da su rika karɓar rahoton yanayi na filin jirgi kafin su tsara ayyukansu, tare da jan hankalin al’umma da su rika bibiyar shafin yanar gizon NiMet domin samun sabbin bayanai.













































