Asusun bada Lamunin Ilimi na Ƙasa (NELFUND) ya amince da sake buɗe shafinsa na Internet na tsawon awanni 48 domin bai wa cibiyoyin ilimi na gaba da sakandare da ba su kammala tantance ɗalibansu ba damar yin hakan.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktar Hulɗa da Jama’a ta Asusun, Mrs. Oseyemi Oluwatuyi, ta fitar a Abuja ranar Juma’a.
Oluwatuyi ta bayyana cewa shafin zai kasance a buɗe daga ƙarfe 12:00 na dare ranar Lahadi, 12 ga Oktoba, zuwa ƙarfe 12:00 na dare ranar Talata, 14 ga Oktoba.
Ta ce wannan ƙarin wa’adin yana da nufin tabbatar da cewa dukkan ɗalibai masu cancanta sun shiga cikin tsarin tantancewa na cibiyoyinsu, a matsayin wani ɓangare na ci gaba da tsarin neman lamunin NELFUND na shekarar karatu ta 2024/2025.
Ta ƙara da cewa cibiyoyin da suka kasa kammala tantancewar a cikin wa’adin da aka kayyade za su rasa damar shiga wannan zagaye na lamuni, wanda hakan zai jefa ɗalibansu cikin rashin samun wannan damar ta lamuni.
Haka kuma, don tabbatar da gaskiya da bin doka, ta ce za a fitar da sunayen cibiyoyin da suka gaza kammala aikin da aka buƙata.
Oluwatuyi ta jaddada cewa NELFUND tana ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da daidaiton samun ilimi ga kowa ta hanyar gudanar da tsarin lamunin cikin gaskiya, inganci da adalci.













































