NDLEA ta kama kilogiram 4,560 na tabar wiwi a wasu jihohin Najeriya

1688920383398
1688920383398

Hukumar da ke Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce jami’anta sun kwace tabar wiwi da nauyinta ya kai kilogiram 4,560 a jihohin Legas da Adamawa da Osun.

Cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Femi Babafemi ya fitar, ya ce jam’ian hukumar sun kuma kai samame wata masana’antar da ake sayar da tabar a jihar Ogun tare da kama mutu hudu da ake zargi da hannu a cinikin tabar ciki har da jami’an wata coci.

Haka kuma sanarwar ta ci gaba da cewa jami’an NDLEA sun kama wata mace bisa zargin safarar ƙwayar fentanyl a birnin Warri, na jihar Delta.

NDLEA ta kuma ce a ranar 5 ga watan Yuli, jami’anta sun kama wata mota ƙirar Hilux ɗauke da tabar wiwi mai yawan gaske da nauyinta ya kai kilogiram 408 a kan hanyar Ngurore zuwa Mayo Belwa a jihar Adamawa, wadda aka yi niyyar safararta zuwa garuruwan Yola da Mubi da kuma Gombe.

Sanarwar ta kuma ce ranar 1 ga watan Yuli jami’an hukumar sun kama buhu 89 na tabar da nauyita ya kai kilogiram 3,842 a jihar Legas da ke kudu maso yammacin kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here