NBA ta yi barazanar ɗaukar matakin raina kotu kan sufeton ƴan sanda da kakakin rundunar kan aiwatar da dokar baƙin gilashin mota

IGP Kayode Egbetokun NEW 680x430

Kungiyar lauyoyin ta ƙasa NBA ta ƙasa ta yi barazanar fara shari’ar raina kotu a kan sufeton ƴan sanda na ƙasa Kayode Egbetokun da kakakin rundunar ƴan sanda CSP Benjamin Hundeyin kan shirin dawo da aiwatar da dokar hana lasisin amfani da baƙin gilashin mota da aka dakatar a baya.

Shugaban ƙungiyar lauyoyin Afam Osigwe ya bayyana cewa ƙungiyar za ta ɗauki wannan mataki idan sufeton ƴan sanda da ya ƙi bin umarnin doka na dakatar da aiwatar da dokar.

Ya kuma jaddada cewa za a ɗauki matakin ladabtarwa na ƙwarewa a kan duk wani lauya da aka samu ya saɓawa kotu.

Martanin ya biyo bayan sanarwar da kakakin rundunar ƴan sanda ya fitar inda ya bayyana shirin fara aiwatar da dokar hana lasisin bakin gilashin mota daga farkon watan Janairu.

Ƙungiyar lauyoyin ta bayyana wannan mataki a matsayin raina kotu da kuma tauye ikon doka, tana tunatar da cewa an ƙaddamar da tsarin ne tun farkon shekarar da ta gabata na neman lasisi ta hanyar internet.

Ƙungiyar ta bayyana cewa an ɗage fara aiwatar da dokar sau da dama bayan korafe-korafe daga jama’a, inda aka samu rahotannin cin zarafi, karɓar rashawa da take haƙƙin ɗan adam, musamman a kan matasa.

Wannan ne ya sa ƙungiyar ta ga dacewar kalubalantar tsarin a gaban kotun tarayya.

Kungiyar lauyoyin ta shigar da ƙara a gaban kotu domin kalubalantar halaccin dokar, tana mai cewa dokar gilashin mota ta samo asali ne daga zamanin mulkin soja kuma ba ta dace da tsarin dimokuraɗiyya da kundin tsarin mulki ba.

Ta kuma bayyana dokar a matsayin haramtacciya da hanyar karɓar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.

Labari mai alaƙa: Ƴan sanda za su ci gaba da aiwatar da dokar lasisin baƙin gilashin mota

Ƙungiyar ta ƙara da cewa rundunar ƴan sanda ba hukuma ce ta tara kuɗaɗen shiga ba, don haka duk wani tsarin da ke tilasta biyan kuɗi yana da matsala.

Ta kuma yi nuni da cewa duk wani mataki na ɓangaren zartarwa da ya saɓa da abin da aka tattauna a kotu na iya zama tauye ikon kotu.

Kungiyar lauyoyin ta yi kira ga Shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya shiga tsakani domin hana dawo da aiwatar da dokar, tana mai cewa hakan zai jefa jama’a cikin ƙarin wahala ta kuɗi.

A gefe guda kuma, rundunar ƴan sanda ta kare matakin da take shirin ɗauka, tana danganta shi da barazanar tsaro da ake dangantawa da motocin da ke da gilashi mai duhu ba tare da izini ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here