Mutane 38 cikin waɗanda aka yi garkuwa da su a jihar Kwara sun shaƙi iskar ƴanci

Eruku Church

Mutane 38 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a Cocin Christ Apostolic da ke Eruku a ƙaramar hukumar Ekiti ta jihar Kwara sun shaƙi iskar ƴanci bayan aikin ceto da aka gudanar.

Wannan na cikin sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan jihar Kwara, Rafiu Ajakaye, ya fitar a ranar Lahadi.

Sanarwar ta bayyana cewa jami’an tsaro da hukumomin tarayya sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da kubutar da mutanen cikin ƙoshin lafiya.

Labari mai alaƙa: Kwara: Ƴan bindiga sun nemi Naira Miliyan 100 a matsayin kuɗin Fansar kowane mutum ɗaya daga iyalan masu ibada da aka sace

Sanarwar ta ce aikin ceton ya haɗa da tsare-tsaren sirri da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro daban-daban domin gano inda masu garkuwa da mutanen suka ɓoye su.

Gwamnatin jihar ta jinjinawa jami’an tsaro bisa jajircewar da suka nuna tun daga lokacin harin har zuwa lokacin da mutanen suka kuɓuta.

Haka kuma, gwamnatocin tarayya da na jihohi da suka ba da gudunmawa sun samu yabo bisa rawar da suka taka wajen ceton mutanen.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakai domin kare rayukan al’umma da tabbatar da tsaro a dukkan sassan jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here