Mun shekara takwas muna ceto yaran da ‘yan bindiga suka sace – Buhari

President Buhari
President Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta shafe shekara takwas tana yunƙurin ceto yaran da ‘yan bindiga suka sace a wurare daban-daban.

Buhari ya bayyana haka cikin saƙonsa na bikin Ranar Yara ta Duniya da ake yi a yau Asabar, yana mai cewa yana jin “raɗaɗin da iyaye ke ji” sakamakon matsalar tsaro da ta jawo yin garkuwa da ɗaliban.

“Kuma ina jin raɗaɗi na rashi, da zaƙuwa, da ɓacin rai da matsalar tsaro ta jawo, wadda muka yi aiki tuƙuru don shawo kanta tsawon shekara takwas,” a cewarsa cikin wasu jerin saƙonni a Twitter.

Ya ƙara da cewa: “Cikin shekara takwas, mun mayar da hankali kan yara wajen tattaunawa da kuma yunƙurin ceto da yawa daga cikinsu bayan an yi garkuwa da su, kuma muka ci gaba da neman inda sauran suke.”

Shugaban ya ce “da ikon Allah sauran da ba a saka ba za su dawo”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here