Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, Shehu Umar Nadada, rundunarsa ta kashe akalla ’yan bindiga 54, yayin da kuma ’yan sanda biyar suka rayuwarsu a shekarar 2022 da ake bankwana da ita.
Nadada ya bayyana haka ne ga manema labarai a taron karshen shekara a ranar Juma’a a hedikwatar rundunar da ke Katsina.
“A ci gaba da yaki da ta’addanci, garkuwa da mutan da satar dabobbi, mun kashe ’yan bindiga 54 a arangama daban-daban, yayin da ’yan sanda biyar suka rasu,” in ji shi.
Ya ce rundunar ta damke mutum 241 da suka daha da ’yan bindiga, masu kai wa ’yan bindiga bayanai da barayin dabobbi, wadanda tuni a cewarsa aka gurfanar da 239 a kotu, yayin da 16 daga ciki ake ci gaba da bincike a kansu.
Kwamishina ya ce rundunar ta kwato dabobbi 1,092, shanu 705, sai tumaki da awaki 370.
Har wa yau, mutum 989 na kotuna daban-daban a fadin jihar suna jiran a yanke musu hukunci kan laifukan da aka gurfanar da su.
“Mun kama ’yan fashi 177 kuma an gurfanar da 169 a kotu, mutum takwas kuma aba ci gaba da gudanar da bincike a kansu.
“Mutum 266 sun shiga hannu kan zargin aikata fyade kuma tuni muka aike da 260 a kotu.”
Kwamishinan ya ce sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda 14, kunshin harsashi 47, bindiga kirar gida 81 da sauran makamai.
Ya gode wa Sufeton-Janar na ’yan sanda da sauran masu ruwa da tsaki na jihar kan yadda suke bai wa sha’anin tsaro muhimmanci.













































