Malami ya ƙalubalanci EFCC, ya roƙi kotu ta soke umarnin ƙwace kadarorinsa na wucin gadi

Abubakar Malami 750x430

Tsohon Ministan Shari’a kuma tsohon Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami, SAN, ya miƙa ƙara gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja inda ya nemi kotun ta soke umarnin wucin gadi na ƙwace kadarori guda uku daga cikin kadarori 57 da Hukumar EFCC ta lissafo domin ƙwacewa ga gwamnatin tarayya.

Malami, wanda ya yi aiki a matsayin Antoni Janar na Tarayya a gwamnatin Muhammadu Buhari, yana ƙalubalantar EFCC kan kadarorin da aka lissafo a matsayin lamba 9, lamba 18 da lamba 48 a cikin buƙatar gaggawa da EFCC ta shigar gaban kotu a ranar 6 ga Janairu.

Kadarorin uku da ake neman a cire daga umarnin ƙwacewa sun haɗa da fili mai lamba 157 da ke Lamido Crescent, Nasarawa GRA a Kano, wanda aka saya a ranar 31 ga Yuli, 2019, ba tare da bayyana adadin kuɗin da aka kashe ba, wanda aka jera a matsayin lamba 9.

Haka kuma akwai gidan kwana da ɗakin ma’aikata a lamba 12, Yalinga Street, Off Adetokunbo Ademola Crescent, Wuse II a Abuja, wanda aka saya a watan Oktoba, 2018 da kuɗi Naira Miliyan 150, da kuma ginin ADC Kadi gidauniyar Malami, wanda aka saya da kuɗi Naira Miliyan 56, waɗanda aka jera a matsayin lamba 18 da lamba 48.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa Mai shari’a Nwite, wanda ya zauna a matsayin alƙalin lokacin hutu, ya bayar da umarnin ƙwace kadarori 57 na wucin gadi a ranar 6 ga Janairu, bisa zargin cewa kadarorin sun samo asali ne daga ayyukan da ba su halatta ba da ake dangantawa da Malami.

Mai shari’a Nwite ya bayar da umarnin ne bayan karɓar buƙatar gaggawa da lauyan EFCC, Ekele Iheanacho, SAN, ya gabatar. Kotun ta kuma umurci EFCC da ta wallafa umarnin a wata jaridar ƙasa domin bai wa masu ruwa da tsaki damar nuna dalilin da ya sa kada a ƙwace kadarorin gaba ɗaya cikin kwanaki 14.

Karanta: Hukumar DSS ta kama tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya Malami bayan fitowarsa daga gidan yari na Kuje

An bayyana cewa kadarorin ƙasa da gine-ginen da darajarsu ta kai Biliyoyin Naira suna a Abuja, Kebbi, Kano da Kaduna.

Sai dai a cikin wata ƙara ta daban da aka shigar a madadin Malami ta hannun ƙungiyar lauyoyi ƙarƙashin jagorancin Joseph Daudu, SAN, tsohon Antoni Janar ya zargi EFCC da samun umarnin wucin gadi ta hanyar ɓoye muhimman bayanai da kuma ba da bayanan da ba su dace ba.

Malami ya roƙi kotu da ta yi watsi da shari’ar domin kauce wa rikice-rikicen hukunci da maimaita shari’a, yana mai cewa matakin na EFCC cin zarafi ne ga haƙƙinsa na mallakar dukiya, haƙƙin ɗaukar sa a matsayin mara laifi, da kuma haƙƙinsa na rayuwa cikin salama tare da iyalinsa.

A cikin buƙatar da aka rubuta a ranar 26 ga Janairu kuma aka shigar a ranar 27 ga Janairu, mai lamba FHC/ABJ/CS/20/2026, Malami ya nemi kotu ta bayar da umarni biyu, ciki har da soke umarnin ƙwace kadarorin lamba 9, 18 da 48, bisa hujjar cewa an riga an bayyana kadarorin a cikin takardun bayyana kadarorinsa a lokacin da yake aiki a matsayin jami’in gwamnati, tare da cewa kadarar lamba 48 na hannun amana ce ga gadon marigayi Khadi Malami Nassarawa.

Haka kuma ya nemi kotu ta hana EFCC ko wakilanta shiga, tsoma baki ko katsalandan ga mallaka, riƙo da iko da kadarorin da ake takaddama a kai.

Lauyan Malami ya jaddada cewa babu wata hujjar farko da ke nuna cewa kadarorin da ake magana a kai sun samo asali ne daga aikata laifi ko wata haramtacciyar hanya, yana mai cewa an bayyana su duka a hukumance ga Hukumar Da’a ta Ƙasa CCB a shekarun 2019 da 2023.

Ya kuma bayyana cewa kadarar lamba 48 na hannun amana ne ga gadon mahaifin Malami marigayi Kadi Malami, tare da cewa hanyoyin samun kuɗin Malami sun haɗa da albashi, alawus, kuɗin kasuwanci, rancen kasuwanci, kyaututtuka daga abokai, da kuma kuɗin da aka samu daga gabatar da littafinsa.

A cewar lauyan, dukkan waɗannan hanyoyin kuɗi suna tabbatar da cewa an mallaki kadarorin ta halastacciyar hanya, don haka umarnin ƙwacewa na wucin gadi ba shi da tushe na shari’a kuma ya dace a soke shi.

Mai shari’a Nwite ya ɗage shari’ar zuwa ranar 27 ga Janairu domin duba rahoton wallafa umarnin, amma shari’ar ba ta ci gaba ba saboda ba a saka ta a jerin shari’o’in ranar ba, sakamakon yadda aka saurari shari’ar a lokacin hutu.

An kuma bayyana cewa akwai wasu lauyoyi da suka shigar da takardu a madadin abokan hulɗarsu domin hana kotu ci gaba da shari’ar ƙwace kadarorin gaba ɗaya.

NAN ta ƙara da cewa Malami na fuskantar tuhumar wankiyar kuɗi daga EFCC, kuma a halin yanzu yana tsare a hannun Hukumar Tsaro ta Farar Hula DSS kan wata shari’a da ta shafi zargin tallafa wa ayyukan ta’addanci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here