Malaman Firamare sun janye yajin aiki a Abuja

3da4ba29 b213 490c 9f4a 1083ae29b94c

Malaman makarantun firaimare da ke Birnin Tarayyar Abuja sun dakatar da yajin aikin baba sai ta gani da suka tsunduma.

Rahotanni sun bayyana cewa tun farkon watan Janairu malaman suka fara yakin aikin, kan rashin biyansu mafi ƙarancin albashi da aka amince da shi na tsawon watanni 25, da kuma gaza aiwatar da kashi 40 cikin dari na alawus-alawus ɗinsu da shugabannin ƙananan hukumomin birnin shida suka yi.

Karanta wannan: Yajin aikin Malamai a Abuja: Wike ya zargi shugabanin kananan hukumomi

Labarin janye yajin aikin na cikin wata sanarwar bayan taro ta haɗin gwiwa da shugaban Ƙungiyar Malamai NUT ta fitar bayan kammala taronta na kwamitin koli da aka yi a Gwagwalada ranar Juma’a da maraice.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here