Majalisar dokokin kasar a ranar Litinin ta mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kudirin dokar zabe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin majalisar dattawa, Sanata Babajide Omoworare ya fitar.
“Akawun majalisar dokokin kasar Mista Olatunde Amos Ojo ya mika sahihan kwafin kudirin dokar zabe na 2022 ga shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari GCFR a ranar 31 ga watan Junairu 2022.
“An yi hakan ne bisa tanadin sashe na 58 (3) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da kuma dokar tabbatar da doka Cap. A2 LFN 2004.
An karanta, “Shugaban ya ki amincewa da dokar zaben 2021 da aka mika masa a ranar 19 ga Nuwamba 2021. Bayan haka Majalisar Dokoki ta kasa ta sake aiki kan Dokar Zabe kuma Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun zartar da haka a ranar 25 ga Janairu 2022.













































