Majalisar dokokin Jihar Rivers ta sake komawa zaman majalisa bayan ƙarewar dokar ta-ɓaci da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kafa a jihar.
Shugaban majalisar, Martin Amaewhule, ya jagoranci zaman ranar Alhamis, 18 ga Satumba, domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi jihar.
Wani kudiri da ’yan majalisa tara suka gabatar ciki har da jagoran majalisa, Major Jack, da Linda Somiari-Stewart da Sylvanus Nwankwo, aka amince da shi.
Kudirin ya bayyana cewa dokar ta-ɓacin ta ƙare ƙarfe 12 na daren Alhamis, abin da ya dawo da dukkan tsare-tsaren dimokuraɗiyya a jihar.
Jagoran majalisar ya bayyana cewa an samu yarjejeniyar zaman lafiya wadda ta kawo daidaito a jihar, tare da jaddada muhimmancin ci gaba da kiyaye zaman lafiyar.
Ya kuma ce ɗaya daga cikin nasarorin dokar ta-ɓacin shi ne gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da aka yi ranar 30 ga watan Agusta, wanda ya samar da shugabannin ƙananan hukumomi 23 da kansiloli.
Majalisar ta gode wa shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa dawo da dimokuraɗiyya a jihar tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da bin sharuddan yarjejeniyar zaman lafiya da kundin tsarin mulkin ƙasa domin kyakkyawan tafiyar da mulki a Rivers.
Haka kuma, majalisar ta umarci gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, da ya aika da jerin sunayen waɗanda zai naɗa a matsayin kwamishinoni a majalisar zartarwa ta jihar. Ta kuma bukace shi da ya fara shirin gabatar da kasafin kuɗi na ragowar shekarar nan domin dacewa da bukatun jama’a.
Baya ga haka, majalisar ta ce za ta binciki duk wata kwangila da kuɗaɗen da aka kashe daga asusun tara kudaden jihar a watanni shida da suka gabata lokacin dokar ta-ɓaci.
Ta ce wannan binciken zai ba da cikakken rahoto kan harkokin kuɗin gwamnati.
Daga ƙarshe, majalisar ta bayyana cewa za ta tsara ajandar dokokinta na ragowar zaman shekarar majalisa ta 10 tare da ba ta ikon ɗaukar duk matakan da suka dace domin tabbatar da nagartaccen mulki da gaskiya a jihar Rivers.













































