Kwamitin raba tallafin kuɗaɗe ga waɗanda gobarar Kasuwar Singer ta shafa a Kano ya tantance ɓarnar da aka yi tare da yin alƙawarin raba tallafin cikin gaskiya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk, ya tabbatar da cewa za a yi rabon kuɗaɗen cikin adalci da gaskiya.
Faruk ya bai wa waɗanda abin ya shafa tabbacin cewa za a kiyaye adalci wajen rabon tallafin da aka ware domin rage musu radadin asarar da suka yi.
Ya jaddada cewa kwamitin zai tabbatar da cewa waɗanda abin ya shafa na gaskiya ne kaɗai za su amfana da tallafin, yana mai cewa gaskiya za ta jagoranci dukkan matakan aikin.
Sakataren Gwamnatin ya roƙi ‘yan kasuwar da su bayar da sahihan bayanai kan asarar da suka yi domin bai wa kwamitin damar gudanar da aikinsa yadda ya kamata.
A cewarsa, sahihan bayanai za su taimaka wajen kauce wa saɓani tare da tabbatar da rabon kuɗaɗen cikin adalci tsakanin waɗanda abin ya shafa.
Shugaban Kasuwar Singer, Alhaji Mohammad Junaid, ya ce an haɗa hukumomin yaƙi da cin hanci da jami’an tsaro cikin kwamitin domin ƙara tabbatar da gaskiya.
ACP Jauro, wakilin Kwamishinan ‘Yan Sanda, ya ce Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya za ta ci gaba da samar da tsaro a Kasuwar Singer domin kare rayuka da dukiyoyi.
A nasa ɓangaren, Alhaji Ado Kurawa ya isar da ta’aziyyar Masarautar Kano ga ‘yan kasuwar da abin ya shafa, tare da kira gare su da su ba kwamitin haɗin kai.













































