Kungiyar Tsofaffin Daliban Kasar Sudan ta nemi ayi adalci ga wadanda rikicin Ad-Damazin ya rutsa da su

People displaced by tribal fighting in Roseiris between Berta and Hausa in thz Blu e Nile state on July 16 2022 768x485 1 750x430 1
People displaced by tribal fighting in Roseiris between Berta and Hausa in thz Blu e Nile state on July 16 2022 768x485 1 750x430 1

Kungiyar tsofaffin daliban kasar Sudan Yan Najeriya (SOSAN) ta bayyana damuwarta kan rikicin baya-bayan nan da ya barke a yankin Ad-Damazin, babban birnin Blue Nile na kasar Sudan, wanda ya yi sanadin kashe-kashe da kuma raba gari tsakanin tsirarun wasu Dalibai da suka kwashe shekaru da dama suna zaman lafiya tare da al’ummar yankin.

Kungiyar ta bayyana wannan lamarin, ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a Kano, ranar Lahadi.

Ta ce rikicin da ba a taba ganin irinsa ba, ya zo da mamaki ga mutane da yawa a ciki da wajen Afirka.

Jaridar Solacebase ta hakaito cewa rikicin kabilanci tsakanin kabilu biyu ya kai har ga kashe mutane da dama a jihar Blue Nile ta Sudan, Ad-Damazin.

Haka Kuma rikicin ya barke ne a yankuna uku da suka hadar da Gaissan da Roseiris da Wad Al-Mahi, biyo bayan kisan da aka yi wa mutum guda sakamakon rashin jituwa tsakanin wasu mutane biyu daga kungiyoyin kabilun biyu.

Har ila yau, an ce lamarin ya faru ne yayin da tashin hankali ya karu baya-bayan nan a yankin bayan kiraye-kirayen amincewa da wata kabila wadda ta fito daga Najeriya amma ta dade a yankin.

Shugaban kungiyar Malam Aliyu Abdulkadir ya bukaci mahukuntan Sudan da su tabbatar da adalci ga wadanda aka zalunta domin shawo kan rikicin.

Abdulkadir wanda mataimakin limamin masallacin Alfruqan ne ya kuma yi kira ga gwamnatin Sudan da ta taimaka wa ‘yan gudun hijirar domin samun agaji da komawa gidajensu don ci gaba da gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.

Ya yi kira ga gwamnatin Kasar nan da Majalisar Dinkin Duniya da su taimaka wa mahukuntan Sudan wajen sake tsugunar da wadanda rikicin ya rutsa da su, tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here