Kungiyar kare hakkin bil’adama, Amnesty International, ta zargi sojojin Najeriya da boye gaskiya kan kisan fararen hula a wasu kauyukan karamar hukumar Silame a Sokoto, yayin wani hari da suka kai kan ‘yan ta’addan Lakurawa a ranar 25 ga Disamba.
Harin ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 10, inda rundunar soji ta ce fashewar wani abu a sansanin ‘yan ta’adda ne ya haddasa lamarin.
Sai dai Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bai wa iyalan wadanda abin ya shafa hakuri.
Amnesty International ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya kafa kwamitin bincike mai zaman kansa don tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa.
Kungiyar ta kuma bayyana damuwa kan yadda hare-haren soji na ci gaba da kashe fararen hula ba tare da daukar matakan kare rayuka ba.