Kano: Kotu ta buƙaci a yiwa Hafsat Chuchu gwajin ƙwaƙwalwa

Hafsat, Chuchu, kotu, gwajin kwakwalwa, kano
Wata babbar kotu da ke zaman ta a Kano ta buƙaci a yiwa Hafsat Surajo (Chuchu) gwajin taɓin hankali a ci gaba da shari’ar da ake yi mata kan zargin kisan...

Wata babbar kotu da ke zaman ta a Kano ta buƙaci a yiwa Hafsat Surajo (Chuchu) gwajin taɓin hankali a ci gaba da shari’ar da ake yi mata kan zargin kisan marigayi Nafi’u Hafiz.

Kotun ta ɗauki matakin ne a daidai lokacin da Hafsat ta ƙi cewa uffan a lokacin da aka karanta mata tuhumar da ake yi mata.

Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Zuwaira Yusuf ta buƙaci a samu likitan ƙwaƙwalwa da zai duba lafiyar Hafsat a inda ake tsare da ita.

Tun farko an karanta wa Hafsat laifukan da ake tuhumar ta da su, sai dai ba ta ce komai ba a lokacin da kotun ta tambaye ta, balle ta iya bayyana abinda ya faru gami da lamarin.

Karanta wannan: An ceto mutum 20 daga hannun masu garkuwa da mutane a Katsina

Yanzu haka dai kotun za ta jira sakamakon gwajin da likita zai yi wa Hafsat kafin ci gaba da sauraron shari’ar.

A cewar kotun, “Dole ne a tantance lafiyar duk wanda ake tuhuma kafin ci gaba da shari’a, kasancewar ba’a yin shari’a da mai taɓin hankali.”

Wannan shi ne karo na farko da aka karanto wa Hafsat tuhume-tuhumen da ake yi mata a gaban babbar kotun.

An gabatar da ita ne a kotun tare da mijinta da kuma wasu mutum biyu da ake zargi da hannu wajen aikata laifin.

Karanta wannan: Hukumar karbar korafi da yaƙi da rashawa ta Kano za ta binciki masu ɓoye kayan abinci

Haka nan a lokacin zaman na yau Alhamis, lauyoyin waɗanda ake tuhuma sun gabatar wa kotu buƙatar bayar da belin mijin na Hafsat da sauran mutum biyun, sai dai kotun ta ce za ta sanya ranar sauraron buƙatar tasu.

A watan Disambar shekarar da ta gabata ne rundunar ƴansandan Kano ta bayyana cewa jami’anta sun kama Hafsat Surajo ƴar shekara 24 da ke Unguwa Uku bisa zargin kashe Nafi’u Hafiz, ɗan shekara 38 a gidanta na aure.

Haka zalika binciken ƴansandan ya kai ga kama mijin matashiyar, Dayyabu Abdullahi mai shekara 38, sai kuma Malam Adamu mai shekara 65 da kuma ƙarin wani mutum ɗaya.

Karanta wannan: “Sauye-sauye 3 da zan samar a hukumar fina-finan Najeriya” – Ali Nuhu

Tun a wancan lokaci ne kotu ta bayar da umarnin ajiye Hafsat a gidan kaso, bayan kammala zaman kotun na yau an mayar da Hafsat da sauran waɗanda ake tuhuma zuwa gidan gyaran hali domin ci gaba da tsare su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here