Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar da umarnin da ya hana Jami’ar Maryam Abacha ta Amurka da ke Nijeriya MAAUN tilasta wa ɗaliban da suka kammala karatu biyan Naira 750,000 a matsayin kuɗin bikin kammala karatu da sharadin fitar da takardun sakamako, shaidar kammala karatu da kuma shigar da su cikin shirin hidimar ƙasa NYSC.
Kotun ta bayyana cewa biyan wannan kuɗi ba zai zama sharadi ba ga waɗannan hakkoki na ɗalibai.
Kotun da Mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ke jagoranta ta kuma umarci MAAUN da ta gaggauta fitar da takardun sakamakon ɗaliban tare da shigar da su cikin shirin NYSC da zarar shafin NYSC ya buɗe, ba tare da ɓata lokaci ba.
Haka kuma, kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 13 ga Janairu 2026 domin sauraron ƙorafin.
Labari mai alaƙa: Jami’ar MAAUN na ƙarkashin bincike yayin da hukumar yaki da cin hanci ta Kano ta dakatar da biyan kuɗin yaye ɗalibai Naira 750,000
Lauyan iyayen ɗaliban, Sagir Sulaiman Gezawa, ya shigar da buƙatar gaggawa ta Ex-parte a gaban kotu domin neman waɗannan umarnai.
Ya kuma shigar da wata buƙata ta daban yana neman kotu ta tantance ko wasiƙar shigar da jami’a da aka bai wa ɗalibai a farkon karatunsu ba ta riga ta nuna sun cika dukkan wajibai da ke kansu ga jami’ar ba, har su kammala karatu cikin sauƙi.
Gezawa ya bayyana cewa ɗaliban sun biya dukkan kuɗaɗen makaranta, sun halarci darussa, sun ɗauki dukkan kwasa-kwasai da suka wajaba, sun rubuta jarabawa kuma sun ci su, don haka bai dace a ɗaure su da wasu ƙa’idoji na waje ba wajen kammala karatu.
Ya ƙara da cewa wajibi ne a kan MAAUN ta fitar da sakamakon ɗalibai tare da shigar da su cikin shirin NYSC.
Rikicin ya samo asali ne bayan MAAUN ta sanya kuɗi Naira 750,000 a matsayin kuɗin abin da ta kira bikin kammala karatu.
Iyayen ɗalibai sun fara ƙin amincewa da kuɗin bisa ganin ya yi tsada matuƙa, amma rikicin ya tsananta ne bayan jami’ar ta fitar da wata sanarwa da ta mayar da biyan kuɗin sharadi kafin a fitar da takardun sakamako da shigar da ɗalibai NYSC.
Bisa ga bayanan wasu iyayen da abin ya shafa, sun ce duk ƙoƙarin su na tattaunawa da mahukuntan makarantar bai haifar da da mai ido ba.
Daga baya, wata sanarwa ta buƙaci biyan kuɗin kafin 30 ga Nuwamba, in ba haka ba za a samu jinkiri wajen kammala karatu, fitar da takardun sakamako da shigar da ɗalibai shirin NYSC.
Sakamakon haka, wani mahaifi daga cikin iyayen daliban ya kai ƙara ga Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano PCACC, wadda ta bayar da umarnin a tsaya matsayin da ake kai har sai an kammala bincikenta.
Daga baya kuma, MAAUN ta samu wani umarnin kotu da ya hana PCACC, gwamnatin jihar Kano, Majalisar Dokokin Jihar Kano, Babban Lauyan Jihar Kano da iyayen da abin ya shafa tsoma baki a harkokin gudanarwa da ilimi na jami’ar, tare da umarnin tsayawa a halin da ake ciki, yayin da aka ɗage shari’ar zuwa ranar 24 ga Disamba 2025 domin ambato.













































