Kungiyar da ke rajin tabbatar da daidaito jihar Kogi (KAP) ta yi kira ga gwamna Ahmed Usman Ododo da ya cika alkawuran da ya dauka a yayin yakin neman zabensa, wajen ganin ya shirya taro domin tattaunawa kai tsaye da ‘yan mazaba don tabbatar da inganta harkokin hidamar jama’a.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar ta KAP Hamza Aliyu ya fitar a ranar Juma’a, ya ce har yanzu ba a kai ga fara shirya irin wadannan taruka da gwamnan ya yi alkawarin gudanar da su ba, wanda hakan ya kawo takaita cudanya da al’umma kai tsaye, inda ya bukaci Gwamna Ododo da ya cika alkawuran yakin neman zabensa.
Kiran na zuwa ne yayin wani taron fahimtar juna da aka gudanar a Lokoja, wanda ya yi nazari kan ayyukan gwamnatin jihar a sassan da suka shafi rayuwar yau da kullum tare da samar da shawarwari masu inganci don inganta ayyukan hidima.
Duk da haka, KAP ta lura cewa gwamnati mai ci ta nuna himma da gaske wajen gudanar da mulki na ‘yan ƙasa ta hanyar tsare-tsare daban-daban.
Karanta: Ta’addanci: An sake kashe mutane 40 a wani sabon harin da aka kai Filato
Haka kuma an amince da cewa yanayin siyasar jihar Kogi ya daidaita, inda aka samu raguwar tashe-tashen hankula idan aka kwatanta da gwamnatocin baya.
Sanarwar ta kuma lura cewa, duk da gagarumin kasafin kasafi na shekarar 2025, yawancin masu ba da ayyuka na gwamnati sun gaza wajen sanya ‘yan kasa.
SolaceBase ta ruwaito cewa, KAP ta ba da shawarar cewa “Dole ne a sake fasalin hukumar kula da shara ta jihar Kogi don aiwatar da ingantaccen tsarin zubar da shara da kuma kafa dabarun zubar da shara a Lokoja da sauran garuruwa.
Gamayyar kungiyar ta jaddada kudirinta na samar da gaskiya da inganta harkokin mulki a jihar Kogi.