Jihar Jigawa ta amince da kashe Naira biliyan 15 a fannin samar da ilimi a matakin farko

Umar Namadi 750x430

Gwamnatin Jigawa ta amince da Naira biliyan 15.8 don gudanar da ingantaccen tsarin ilimi a matakin farko na don bunkasa samar da ilimi mai inganci kyauta a jihar.

Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu, Sagir Musa ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Dutse.

Ya ce Majalisar zartaswa ta Jiha (SEC) ta amince da fitar da kudin domin a gaggauta aiwatar da shirin a Jihar Jigawa wanda aka tsara shi don ƙarfafa tura sabbin fasahohin zamani da kuma hanyar da ake amfani da bayanai don samar da ingantattun kayan koyo a kakar karatu ta 2024-2026.

Karin karatu: Barau ya yabawa Tinubu kan sauya sunan Jami’ar Ilimi ta tarayya Kano zuwa jami’ar Yusuf Maitama Sule

Musa ya kuma ce, majalisar ta kuma amince da bayar da gudunmawar Naira miliyan 839 ga iyalai 210 da fashewar tanka ta Majiya ta shafa.

Kwamishinan ya ce hukumar ta SEC ta kara amincewa da ci gaba da aiwatar da shirin lafiya mai taken Alternative Care for Children (ACC), don tabbatar da kare lafiyar mutane masu rauni da yara. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here