Jami’an ceto sun fito da gawarwakin mutum biyu daga cikin ginin da ya ruguje a Lagas

LASEMA 750x430 1
LASEMA 750x430 1

Jami’an hukumar ba da agajin gaggawa sun gano gawarwaki biyu daga baraguzan ginin da ya ruguje da sanyin safiyar Lahadi a Unguwar Lekki dake jihar Legas.

Ko’odinetan hukumar na shiyyar kudu maso yamma, Ibrahim Farinloye, ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Lahadi a Legas.

Farinloye, ya ce ginin mai hawa bakwai da ake ginawa ya ruguje ne a titin Oba Idowu Oniru dake yankin Lekki.

Ya ce yanzu haka ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto sauran mutanen da suka makale a karkashin baraguzan ginin.

Jami’an da suka kai daukin gaggawa a wurin da lamarin ya faru sun hada da rundunar ‘yan sanda da hukumar NEMA, da Kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas (SEMA) sai hukumar kashe gobara ta jihar da kuma hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here