Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta ƙasa JAMB ta sanar da cewa mutane masu buƙata ta musamman za su samu takardun neman rubuta jarabawar shiga manyan makarantu ta UTME kyauta domin shekarar karatu ta 2026 zuwa 2027.
Sanarwar ta fito ne a cikin mujallar mako-mako ta hukumar wadda aka wallafa a shafin internet ɗinta.
Wannan shiri na cikin manufofin bai wa kowa dama a fannin ilimi na hukumar, kuma za a aiwatar da shi ne ta hannun ƙungiyar ba da dama daidai ga kowa ta hukumar ga ɗaliban da suka cancanta waɗanda ke shirin rubuta jarabawar UTME ta shekarar 2026 zuwa 2027.
Magatakardar hukumar JAMB ta ƙasa, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da masu ruwa da tsaki a hedikwatar hukumar da ke birnin Abuja.
Ya jaddada ƙudurin hukumar na ci gaba da tallafa wa masu buƙata ta musamman tare da tabbatar da cewa babu wani ɗalibi da ya cancanta da za a hana shi damar shiga manyan makarantu sakamakon matsalar jiki ko ta fahimta.
Masu cin gajiyar wannan shiri sun haɗa da ɗaliban da ke fama da cututtuka irin su Galahanga, da ciwon Autism, da masu lalaurar rashin iya karatu da rubutu da kuma masu rauni wajen iya sarrafa jikinsu.
Hukumar ta bayyana cewa duk masu nakasa da ke son cin gajiyar takardun UTME kyauta dole ne su mallaki aƙalla kiredit biyar a sakamakon sakandare O’Level, kuma ba fiye da zama biyu ba.
Haka kuma hukumar za ta samar da littattafan sauti ga masu lalurar gani domin sauƙaƙa samun ilimi, inda littattafan ke kasancewa nau’in dijital da aka sauya daga rubutattun littattafai, kuma za a samar da su a tsarin sauti irin su MP3, WMV da WMA.
Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana cewa wannan shiri ya yi daidai da manufar hukumar ta adalci, daidaito da bai wa kowa dama a tsarin karɓar ɗalibai a Nijeriya, tare da tabbatar da ci gaba da kula da jin daɗi da nasarar masu buƙata ta musamman.













































