Izinin sanya baƙin Gilashin Mota: Ƙungiyar Lauyoyi ta maka babban sufeton ƴan sanda a kotu

Tinted Cars

Ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta shigar da babban sufeton ‘yan sanda na kasa, Kayode Egbetokun a gaban kotu, tana kalubalantar sabuwar manufar ba da izinin gilashin da aka bullo da ita, wadda ta bayyana a matsayin haramtacciyar hanya da take hakkin ‘yan kasa.

A taron Majalisar Zartaswa ta kasa (NEC) da ta gudanar a Enugu a ranar 23 ga watan Agusta, kungiyar ta yanke shawarar yin adawa da manufar, wacce aka bullo da ita a watan Afrilun 2025 kuma ta bukaci masu ababen hawa su rika samun takardar izinin sanya baƙin gilashin ta hanyar hanyar sadarwa ta zamani (possap.gov.ng).

Manufar, wacce aka shirya za ta fara aiki tun daga ranar 1 ga watan Yuni amma aka dage zuwa ranar 2 ga watan Oktoba, ta janyo suka kan damuwar da ake da ita dangane da ita da kuma bin doka.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Paul Ananaba, SAN, shugaban sashin kula da sha’awar jama’a da ci gabansu (SPIDEL) na NBA, ya ce umarnin ya haifar da ayar tambaya kan yadda za a bi.

Karin karatu: IGP ya gayyaci mai magana da yawun gwamnan Kano bisa ƙorafin Ganduje

Ya ce, adreshin internet da aka ƙaddamar don aiwatarwa ana gudanar da shi ta hanyar dillalai masu zaman kansu, ba tare da wata shaida da ke nuna cewa kudaden shiga da aka samu daga manufofin za a tura su cikin Asusun Tarayya ba.

Hukumar ta NBA ta kuma yi zargin cewa tun ma kafin a fara aiwatar da dokar, an samu rahotannin cin zarafi da karbar kudin jama’a a shingayen binciken ‘yan sanda.

Har ila yau, ta yi iƙirarin cewa ana biyan kuɗin izinin zuwa wani asusun sirri na Parkway Projects, maimakon a cikin Asusun Tarayya ko Asusun Baitulmali (TSA).

Ananaba ya ce kungiyar ta kudiri aniyar ci gaba da gudanar da shari’ar har zuwa karshe, sannan ta bukaci ‘yan sanda da su dakatar da aiwatar da dokar har sai kotu ta yanke hukuncin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here