Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta hasashen kashe Naira Biliyan 873,778,401,602.08 don gudanar da babban zaɓen 2027.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan yayin gabatar da kasafin kudin hukumar na 2026 da cikakken bayani kan kudin gudanar da zaɓen 2027 a gaban Kwamitin Haɗin Gwiwar Majalisar Dokoki kan Al’amuran Zabe.
Bayani kan kasafin ya nuna cewa Kudin Gudanar da Zaɓe ya kai Naira 375,748,195,271.47, yayin da Kudin Gudanarwa na Zaɓe ya kai Naira 92,311,591,396.58.
Hukumar ta kuma yi hasashen Naira 209,205,589,977.70 don Kudin harkokin Fasahar Zaɓe, wanda ya haɗa da tsarin lantarki da kayan aikin da suka shafi shi.
Bugu da kari, Kudin Manyan Abubuwan Zaɓe an kiyasta Naira 154,904,529,641.94.
Wadannan abubuwa hudu sun kai a kashe musu Naira 832,169,906,287.69.
INEC ta haɗa da Kudin Sauran Abubuwa da ya kai Naira 41,608,495,314.39, wanda ya kawo Jimillar Kudin babban Zaɓen 2027 zuwa Naira Biliyan 873,778,401,602.08.
Farfesa Amupitan ya fayyace cewa kasafin zaɓe ya bambanta da kasafin da hukumar ta bayar na Naira Biliyan 171 don shekarar kudin 2026, wanda aka tanadar don gudanar da ayyukan yau da kullum, ciki har da zaben rarraba kujeru da zabe a wasu lokuta.
Ya ce gabatarwar ta bi Sashe na 3(3) na Dokar Zaɓe ta 2022, wanda ke bukatar hukumar ta gabatar da kasafin zaɓe a kalla shekara guda kafin zaɓen.
Yayin zaman, ‘yan majalisar sun nuna damuwa kan hanyoyin samun kudade da aiwatar da muhimman tanade-tanade na Dokar Zaybe da aka gyara, musamman yadda za a aika sakamakon zabe ta lantarki.
Shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwar kan Al’amuran Zabe, Sanata Samuel Lalong, ya ce Majalisar Dokoki za ta duba kasafin sosai kafin amincewa da abin da ta ga ya dace don gudanar da zaɓe cikin sauki a fadin kasa.
Kwamitin ya nuna shirin sake duba tallafin kudi ga mambobin yan yiwa Kasa hidima (NYSC) da za a tura don aikin zaɓe, bayan bukatar da shirin ya yi na karin tallafin kudi.
A karkashin wannan shiri, kowanne memba zai samu Naira 127,000, tare da Naira 4,500 don abinci da Naira 5,000 don horo na tsawon kwanaki biyar.
Ana sa ran kusan membobin NYSC 450,000 za su kasance cikin aikin babban zaɓen 2027.













































