INEC ta buga sunan Shekarau a matsayin Dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya na Jam’iyyar NNPP

Ibrahim Shekarau new
Ibrahim Shekarau new

Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta bayyana sunan Ibrahim Shekarau a matsayin dan takarar Kano ta tsakiya a jam’iyyar NNPP, duk da cewa ya fice daga jam’iyyar kusan wata guda da ya gabata.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Sanata Ibrahim Shekarau, ya bayyana ficewarsa a hukumance daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar PDP, tun a ranar 29 ga watan Agustan da ya gabata.

Hakan ya faru ne yayin da Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta fitar da sunayen Yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Godswill Akpabio a matsayin dan takarar Sanatan Mazabar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma, na Jam’iyyar, amma kuma ta cire sunan shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, Wanda Shima dan takarar Sanatan Yobe ta Arewa ne.

Hakan dai na zuwa ne duk da rahotannin da ke cewa jam’iyyar ADC mai yiwuwa ta dakatar da dan takararta na shugaban kasa, Dumebi Kachikwu.

Sai dai a taronta na mako-mako da ta saba gudanarwa hukumar, ta amince da jerin sunayen ‘yan takarar na karshe kamar yadda sashe na 32(1) na dokar zabe ta 2022 da sashi na 8 na Jadawalin Zaben Kasa.

Kwamishinan INEC na kasa mai kula da kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe, Barrister Festus Okoye, ya bayyana cewa buga cikakken sunaye da adireshi na duk ‘yan takarar da aka zaba ya biyo bayan yadda jam’iyyun siyasa suka gudanar da zaben fidda gwani.

“Bayan haka, ba a yarda a janye ko musanya ’yan takara ba sai dai idan mutum ya mutu kamar yadda aka tanada a sashe na 34 (1) na dokar zabe ko kuma bisa umarnin kotun da ta dace,” inji shi.

A cewarsa, jerin sunayen da aka buga a yanzu ya kunshi sunayen ‘yan takarar da aka tantance masu inganci a zaben kasa a karshen zaben fidda gwani na jam’iyyar da kuma lokacin da aka ware na janyewa da sauya ’yan takara.

Ya ce za a buga jerin sunayen karshe na ‘yan takarar zaben Jihohi (Gwamna da Yan majalisar Jihohi) a ranar 4 ga Oktoban 2022 kamar yadda aka riga aka nuna a kan Jadawalin Babban Zaben 2023.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here