ICPC ta tabbatar da karɓar ƙorafin Dangote kan shugaban hukumar NMDPRA, ta ce za a bincika ƙorafin yadda ya dace

dangote icpc faruk2

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka masu alaƙa da shi ta ƙasa ICPC ta tabbatar da karɓar ƙorafi a hukumancw da aka shigar kan babban daraktan hukumar kula da harkokin man fetur da ƙayyade farashi ta ƙasa NMDPRA, Alhaji Farouk Ahmed.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ICPC, John Okor Odey, ya sanya wa hannu, inda ya bayyana cewa an karɓi ƙorafin a ranar Talata.

Sanarwar ta bayyana cewa ɗan kasuwa Alhaji Aliko Dangote ne ya shigar da ƙorafin ta hannun lauyansa, kuma hukumar ta karɓe shi a hukumance a ranar da aka gabatar da shi.

Hukumar ICPC ta bayyana cewa za ta gudanar da cikakken bincike kan ƙorafin bisa tanadin dokoki da ikon da doka ta ba ta, tare da tabbatar wa al’umma cewa za a bi ka’idojin doka yadda ya kamata.

Labari mai alaƙa: Dangote ya shigar da ƙorafi ga ICPC, yana neman ta kama shugaban hukumaar NMDPRA kan zargin cin hanci

Sanarwar ta ƙara da cewa za a binciki ƙorafin ba tare da nuna son kai ba, ko da yake ba ta shiga bayanin zarge-zargen da ke ƙunshe a cikinsa ba.

A cewar bayanan da suka gabata, Dangote ya buƙaci a kama tare da bincikar Ahmed, yana zarginsa da rayuwa sama da albashinsa a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati, inda ya yi zargin kashe sama da Dala Miliyan Bakwai wajen biyan kuɗin karatun ’ya’yansa huɗu a makarantu daban-daban a ƙasar Switzerland tsawon shekaru shida.

Ƙorafin ya kuma zargi shugaban NMDPRA da karkatar da kuɗaɗen jama’a domin amfanin kansa da biyan buƙatun rayuwa ta sirri, yana mai jaddada cewa dukkan kuɗaɗen da ya samu a tsawon aikinsa a gwamnati ba su kai wannan adadi ba.

H aukumar ICPC ta sake jaddada aniyarta ta tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here