Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet ta bayyana cewa za a samu hazo na ƙura a sassa daban-daban na Najeriya daga ranar Laraba zuwa Juma’a.
Hasashen yanayin da hukumar ta fitar a birnin tarayya Abuja ya nuna cewa a ranar Laraba, za a samu matsakaicin hazo na ƙura a yankin Arewa, inda nisan ganin ido a kwance zai kai tsakanin kilomita biyu zuwa biyar.
Rahoton ya nuna cewa za a samu raguwar ganin ido zuwa ƙasa da ko kuma daidai da mita dubu ɗaya a wasu sassan jihohin Katsina, Kano da Jigawa a duk tsawon lokacin hasashen.
Hukumar ta kuma yi hasashen samun matsakaicin hazo na ƙura a yankin Arewa ta Tsakiya a duk tsawon lokacin da rahoton ya shafa.
A yankin Kudu kuwa, hukumar ta bayyana cewa za a ga sararin samaniya mai haske tare da ɗan gajeren gajimare, inda ake sa ran samun ƙananan hadari da tsawa da ruwan sama kaɗan da rana ko da yamma a wasu sassan jihohin Legas, Bayelsa, Delta, Rivers, Cross River da Akwa Ibom.
Hukumar ta ƙara da cewa a ranar Alhamis, za a ci gaba da samun matsakaicin hazo na ƙura a yankunan Arewa da Arewa ta Tsakiya, yayin da a yankin Kudu za a ga sararin samaniya mai haske tare da ɗan gajeren gajimare, kuma akwai yiwuwar samun ƙananan hadari da tsawa da ruwan sama kaɗan a jihohin Ondo, Bayelsa, Rivers, Delta da Edo daga bisani a rana.
A ranar Juma’a, hukumar ta yi hasashen samun ɗan ƙaramin hazo na ƙura a yankin Arewa, yayin da za a ci gaba da samun matsakaicin hazo a yankin Arewa ta Tsakiya, sannan a yankin Kudu za a ga sararin samaniya mai haske tare da ɗan gajeren gajimare da yiwuwar samun ƙananan hadarin tsawa da ruwan sama kaɗan a jihohin Legas, Edo, Delta da Bayelsa.
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta gargaɗi jama’a cewa ƙurar za ta ci gaba da kasancewa a sararin samaniya, tare da ba da shawarar ɗaukar matakan kariya, musamman ga masu fama da cututtukan numfashi kamar asma, inda ta kuma shawarci direbobi su yi taka-tsantsan yayin tuki a lokacin ruwan sama.
NiMET ta yi kira ga kamfanonin jiragen sama su rika samun rahotannin yanayin jiragen sama kai tsaye daga hukumar domin tsara ayyukansu yadda ya kamata.
NAN












































