Hukumar ƙwallon Tennis ta Najeriya ta zaɓi Yusuf Datti a matsayin mataimakin shugabanta na ƙasa

IMG 20251026 WA0014 1 750x430

Hukumar ƙwallon Tennis ta Najeriya ta zaɓi daraktan gasar Tennis ta Kano Dala Hard Courts, Alhaji Yusuf Datti, a matsayin mataimakin shugabanta na ƙasa domin cika wa’adin shekaru huɗu masu zuwa.

An gudanar da zaben ne ƙarƙashin kulawar hukumar wasanni ta ƙasa a Kaduna a watan Satumba, inda Datti ya fito a matsayin wakilin yankin Arewa maso Yamma a hukumar.

Haka kuma, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Delta, Victor Ochei, ya lashe zaben shugaban ƙasa na hukumar bayan samun rinjayen kuri’u a zaben da aka gudanar a Package B na filin wasa na Moshood Abiola, Abuja, ranar Asabar.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, Yusuf Datti wanda yake rajistra  na jami’ar Khalifah Isyaku Rabiu (KHAIRUN), ya samu kuri’u 12 daga cikin 14 da aka kada don zama mataimakin shugaban ƙasa, yayin da Victor Ochei ya samu 11 ya zama shugaban ƙasa na hukumar Tennis ta Najeriya.

Datti ya gode wa mambobin hukumar bisa amincewar da suka nuna gare su, tare da jinjinawa shugaban hukumar wasanni ta ƙasa, Alhaji Shehu Dikko, da darakta janar ɗinta, Mista Olapade, bisa jajircewarsu wajen bunƙasa harkokin wasanni a ƙasar.

Ya kuma kira kamfanoni, masu kuɗi da ‘yan siyasa da su haɗa kai da hukumar don cigaban wasan Tennis a Najeriya, tare da gode wa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu bisa jajircewarsa wajen tallafa wa ci gaban wasanni a ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here