Gwamnoni zasu yi wata ganawa ranar Laraba kan batutuwan Tattalin Arziki da Kuma Tsaro

NGF 727x430 1
NGF 727x430 1

Gwamnonin jihohi 36 a karkashin kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) za su gana ranar Laraba a Abuja domin tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arziki da matsalolin tsaro da sauran kalubalen da ke addabar al’ummar kasar.

Mista Abdulrazak Bello-Barkindo, Daraktan Yada Labarai na Kungiyar gwamnonin NGF shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja.

Ya ce a nasa ran yanayin tattalin arziki ne zai mamaye agendar tattaunawar, idan gwamnoni 36 zasu hadu a dakin taro na Banquet Hall dake fadar shugaban kasa a Abuja.

Ya yi watsi da cewa ba gaskiya ba ne, rahotannin da wasu kafafen yada labarai a baya-bayan nan ke fitarwa na cewa gwamnonin sun bai wa shugaban kasa shawara da ya tilasta wa ma’aikatan gwamnati masu shekaru 50 zuwa sama ritayar dole.

A cewarsa, taron zai kasance na farko a wannan Shekarar ta 2022 da gwamnonin za su yi tare a kan tattalin arzikin kasa.

so
Bello-Barkindo ya ce gwamnonin za su kaddamar da asusun kula da lafiya a matakin farko da kuma tsarin bankin duniya SFTAS kafin su shiga taron, wanda ake sa ran za a fara da karfe biyu na rana.

Ya kara da cewa gwamnonin za Kuma su sami sabbin bayanai game da shirin farfadowa da tattalin Arzikin Kasa bayan cutar Corona wato (COVID-19 Action Recovery and Economic Stimulus Programme) yayin taron.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here