Gwamnatin tarayya ta kafa cibiyoyin koyarwa 119 a fadin ƙasar domin bunƙasa damar samun ilimi a matakin farko ga almajirai da sauran yaran da ba sa zuwa makaranta, tare da mayar da tsarin karatun almajirci cikin sahun karatun da ake tallafawa kamar sauran makarantu.
Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Ilimin Almajirai da Yaran da basa zuwa Makaranta ta ƙasa, Nura Muhammad, ya bayyana cewa cibiyoyin suna aiki ta hanyoyi biyu, inda wasu ke tallafawa makarantu na almajirai da darussan karatu da lissafi, yayin da wasu ke koyar da yaran da ba sa zuwa makaranta ta tsarin hanzarta ilimi na ABEP.
Ya ce tsarin ya ba wa yaran damar kammala ilimi a matakin farko cikin gajeren lokaci, tare da tabbatar da cewa almajirai ba za a sake rarrabe su matsayin yaran da ba sa zuwa makaranta ba, domin yanzu za su samu tallafi da matsayin daidai da sauran makarantu.
Ya ce hukumar ta kafa ofisoshi a dukkan jihohi cikin watanni 28 tun bayan kafuwarta, tare da kaddamar da kamfen na wayar da kan jama’a daga unguwa zuwa unguwa a jihohi bakwai da suka haɗar da Kano, Jigawa, Yobe, Borno, Legas, Ogun da Kuros Riba domin jan hankalin iyaye da shugabanni kan muhimmancin saka yara makaranta.
Karanta: Ministan Abuja ya dakatar da sakataren Ilimi kan fitar da takardar umarnin rufe makarantu
Muhammad ya ce matakan suna kan hukumar da dokar kafa hukumar da majalisar dokoki ta ƙasa ta amince da ita, wadda shugaban ƙasa ya rattaba hannu a kai a Mayun 2023 domin sake fasalin tsarin almajirci ta hanyar ilimi, lissafi da koyon sana’o’i ga miliyoyin yara.
Ya ce sakataren zartarwa na hukumar, Muhammad Idris, ya gudanar da muhimman tattaunawa da manyan shugabanni na ƙasa, wanda hakan ya kai ga tarukan Abuja guda biyu da suka samar da tsare-tsaren hukumar na shekaru goma (2025–2035).
Daga cikin manyan shirye-shiryen hukumar akwai cibiyar koyon sana’o’in na Tinubu da aka kafa domin hada ilimin addini da koyon sana’o’in zamani, inda dalibai a Kaduna suka yi watanni tara suna koyon karatun Larabci da Turanci, fassarar Alƙur’ani da kuma sana’o’i irin su aikin gine-gine, noma, gyaran wayoyi da ICT.
A rassa irin na Ibadan kuwa, ‘yan mata 150 suna samun horo domin ci gaba da karatunsu bayan shirin.













































