Gwamnatin jihar Kano ta kammala tare da miƙa wani muhimmin aikin magudanar ruwa a garin Toranke da ke ƙaramar hukumar Ajingi, wanda ya kawo ƙarshen ambaliyar ruwa da ta daɗe tana janyo asarar rayuka, lalata gidaje da gonaki a yankin tsawon shekaru.
Wannnan cikin wata sanar da Kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar Kano, Dakta Dahir Muhammad Hashim ya fitar, inda ya bayyana cewa an aiwatar da aikin ne da amincewar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a matsayin wani ɓangare na kudurin gwamnatin jihar na kare rayukan jama’a, dukiyoyinsu da muhimman ababen more rayuwa a faɗin Kano.
Sanarwar ta nuna cewa aikin magudanar ruwan ya samar da sauƙi mai dorewa ga al’ummar Toranke, waɗanda a baya suke fuskantar ambaliyar ruwa a duk lokacin damina, lamarin da ke haddasa mutuwar mutane da kuma babbar asarar dukiya.
Bayan kammala aikin, yankin ya samu ruwan sama a bana ba tare da samun rahoton mutuwa ko lalacewar dukiya ba, abin da ya nuna nasarar aikin da kuma ingancinsa wajen magance matsalar ambaliya a yankin.
Karanta: Gwamnatin Kano za ta gudanar da ƙidayar cibiyoyin karatun gaba da sakandare a faɗin jiha
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa aikin na nuna aniyar ta wajen gina ingantattun ababen more rayuwa masu ɗorewa, tare da ɗaukar matakan rigakafi kan matsalolin da sauyin yanayi ke haddasawa, musamman waɗanda ke da alaƙa da ambaliyar ruwa da zaizayar ƙasa.
A lokacin miƙa aikin, an wayar da kan mazauna yankin kan muhimmancin kula da magudanan ruwa, musamman guje wa zubar da shara, toshe hanyoyin ruwa ko gina gine-gine a kansu, domin tabbatar da dorewar aikin da kariya ga al’umma.
A matsayin godiya, al’ummar Toranke sun sanya wa hanyar da aka gyara suna Gidan Abba Kabir Yusuf, yayin da gwamnatin jihar ta ce za ta ci gaba da bai wa haɗin gwiwar al’umma muhimmanci a aiwatar da ayyukan ci gaba masu ɗorewa a faɗin jihar Kano.













































