Gwamnnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce zai mayar da ginin shatale-talen ƙofar gidan gwamnati da ya rusa, zuwa Na’ibawa dake gefen garin Kano.
Kakakin gwamnan, Hisham Habib ya sanar da cewa gwamnan da kansa ya kai matar da ta zana ginin, Kaltume Gana zuwa in da za a sake sabon ginin.
Gwamnan ya ce wurin ya dace da ginin kasancewar ya na bayan gari kuma ba zai haifar da irin ƙalubalen da ya haifar a baya ba.












































