Gwamna El-Rufai ya amince da bada miliyan 18 ga iyalai 9 da suka rasu a harin jirgin ƙasa

El Rufai signs 768x463 1
El Rufai signs 768x463 1

Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da bayar da Naira miliyan goma sha takwas ga iyalan mutane tara da aka kashe a harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna da ‘yan ta’adda suka kai.

Babban sakataren hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Kaduna KADSEMA Malam Muhammed Mukaddas, ne ya bayyana hakan da yammacin yau Laraba a Kaduna.

Ya ce, Gwamna Nasir El-Rufa’i a jiya 19 ga watan Afrilu ya amince da raba Naira miliyan biyu ga kowanne iyali waɗanda suka mutu a harin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna.

Mukaddas ya ce, gwamnan ya kuma amince da bayar da Naira 250,000 ga mutane 22 kowannensu waɗanda suka samu munanan raunuka yayin harin.

Babban sakataren hukumar ta KADSEMA, ya ce ba wai an bada kuɗin don biyan diyya ne ga wadanda abin ya shafa ba, sai dai don tallafa musu.

Haka kuma ya ce, a matsayin hukumar na yin aikin jin kai, aikinta shi ne ta kasance cikin masu ba da agajin gaggawa a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.

Haka kuma ya ƙara da cewa “An kira waɗanda abun ya shafa su 369 kuma an ba su damar samun tallafi, kuma mutane 264 sun yarda da tayin kuma an tallafa musu,” in ji sakataren zartaswar.

Mukaddas ya ƙara da cewa, a lokacin da lamarin ya faru, nan take hukumar ta sanar da manyan jami’an gwamnati, sannan ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su shiga aikin bincike, ceto da kwashe mutanen da lamarin ya rutsa da su.

“Mun tanadi motocin ɗaukar marasa lafiya don kwashewa kuma muka komawa wurin da lamarin ya faru, Kafin isowar sojoji tuni mun fara kwashe gawarwakin da kuma waɗanda suka samu munanan raunuka da kuma mutum ɗaya da ya tsere daga hannun su ɓata garin.

“Mun ajiye wadanda suka mutu a NARH 44 da wasu a asibitin St. Gerald domin samun kulawa. Mun kafa wata cibiyar bincike wadda ta bai wa iyalan waɗanda abin ya shafa damar yin kira da a yi bincike tare da bayar da bayanan da suka dace game da ƴan uwansu da suka ɓace,” inji shi.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewa, idan za a iya tunawa a ranar 28 ga watan Maris ne wasu ƴan bindiga suka kai hari kan wani jirgin ƙasa wanda ke tafiya daga Abuja zuwa Kaduna, inda suka kashe fasinjoji akalla takwas tare da jikkata wasu da dama, yayin da wasu da har yanzu ba a tantance adadinsu ba.

Harin dai ya zo ne bayan harin da aka kai a filin jirgin Kaduna, wanda ya kai ga rufe shi.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here