Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Umarci A Gaggauta Gyara Asibitin Sir Sunusi.

IMG 20230921 170314

A kokarin sa na ingantaccen tsari a fagen cigaban kiwon lafiya a kano kamar yadda yake kunshe cikin kundin manufofin sa, Gwamna Abba kabir Yusuf ya bada umarnin a gaggauta gyara babban asibitin Sir Sunusi dake nan kano.

Gwamnan ya bayyana haka ne jim kadan da kai wata ziyarar ba-zata zuwa asibitin akokarin nazarin lalubo hanyoyin inganta kiwon lafiya ga alummar kano.

Cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya rabawa manema labarai a kano.

Gwamnan ya nuna takaici kan halin tabarbarewa da asibitin ya lalace, Inda nan take ya bada umarnin fara aikin gyare gyaren domin tabbatarwa da majinyata da ma’aikatan lafiya sun samu yanayi me kyau da ya dace a asibitin.

“Tabbas banji dadi kuma dole a dauki mataki na kawowa asibitin dauki, saboda abin da na gani da idona ya ban tsoro sosai da sosai, ina so in tabbatar muku da cewa gwamnatin mu za ta kawo muku agaji nan bada jimawa ba.

“Zan umurci ma’aikatar lafiya da dukkan hukumomin da ke karkashinta da su shirya yadda za a gudanar da aikin gyaran dakunan kwanan marasa lafiya, bandakuna da dakunan yin tiyata” in ji Gwamna Abba Kabir.

Gwamnan ya kuma bayar da umarnin a gaggauta daukar wata ma’aikaciyar lafiya ta wucin gadi mai suna Khadija Adam, Saboda irin kwazon da take na tallafawa marasa lafiya.

Ya kuma yi wa marasa lafiya dake asibitin fatan samun sauƙi, tareda bada kyautar naira dubu ashirin ga kowanne mara lafiya dake asibitin a matsayin tallafin gaggawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here