Gbajabiamila zai gana da Manyan jami’an gwamnatin Tarayya bayan ganawa da ASUU

Reps meet ASUU
Reps meet ASUU

Shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, ya gayyaci wasu manyan jami’an gwamnati zuwa wani taro da nufin sasanta rikicin dake tsakanin gwamnati da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da ke ci gaba da gudana.

Gbajabiamila ya bayyana haka ne bayan wata ganawar sirri da shugabannin majalisar suka yi da kungiyar ASUU na tsawon sa’o’i biyar ranar Talata a Abuja.

Wadanda aka gayyata sun hada da, Akanta Janar na Tarayya da Odita Janar na Tarayya da Darakta Janar na Hukumar NITDA da takwaransa na Hukumar Kula da albashin Ma’aikata da Kudaden Shiga ta Kasa.

Ya ce jami’an gwamnatin za su bayyana a ranar Alhamis, 22 ga watan Satumbar nan don kammala tattaunawa da nufin gabatar da yarjejeniyar ga shugaban kasa Muhammadu Buhari domin amincewa da aiwatar da ita.

Shugaban majalisar ya ce an samu ci gaba mai ma’ana, inda ya ce majalisar na shirin yin mu’amala kai tsaye da ASUU a matsayin bangaren gwamnati mai zaman kansa domin gano bakin zaren warware matsalar.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya yabawa shugaban majalisar kan saka baki a yajin aikin da ake ci gaba da yi.

Ya bayyana matakin a matsayin ci gaba mai kyau, yana mai cewa kungiyar za ta jira sakamakon ganawar da za a yi da manyan jami’an gwamnati.

Osodeke, ya ce la’akhari da tasirin ganawar da aka yi da shugaban majalisar, yana fatan nan gaba kadan za a warware matsalolin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here