FIFA za ta fara amfani da harshen Labarci a matsayin harshenta na 5

21DC1C85 D016 45D2 AC91 EFE601F5AAFB
21DC1C85 D016 45D2 AC91 EFE601F5AAFB

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta shirya tsaf domin sanya harshen larabci a matsayin harshe na 5 da hukumar ke amfani da shi, inda harshen na larabci zai biyo bayan Ingilishi da Faransanci da Jamusanck da kuma Sfaniyanci.

FIFA ta bayyana hakan ne cikin wani sanarwa  da ta wallafa a shafin ta na Intanet.

Sanarwar ta ce shugaban hukumar ta FIFA Gianni Infantino ne ya bayyana hakan a yayin taron ranar harshen harshen larabci ta duniya tare kaddamar gasar FIFA Arab na shekarar 2021 a kasar Qatar.

Ya ce dama can hukumar ta dade ta shirye-shirye kan wannan batu, kwatsam sai gashi an shirya wannan gasar wadda zata hada kungiyoyin kwallon kafa na kasashe 23 dake gasar ta tsakiya, wanda hakan zai taimaka wajen aiwatar da kudirin FIFA na sanya harshen larabci cikin jerim harsuna da take amfani dasu.

Ya ce larabci yana da muhimmanci kware da gaske duba da cewa sama da mutane miliyan 450 ne a fadin duniya suke magana da harshen, inda yake a matsayin  babban yare a sama da kasashe 20.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kasar kasar ke shirin karbar bakuncin gasar cin kofin Duniya na shekarar 2022.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here