Duk ƴan sandan da suka kasa rubuta jarabawar ƙarin girma sau uku za a tilasta musu yin ritaya – PSC ta yi gargaɗi

Police exams

Hukumar kula da ayyuka ƴan sanda (PSC) ta bayyana cewa jami’an ‘yan sanda 30 na manyan mukamai sun shiga jarabawar karin girma a matsayin wani bangare na ci gaban aikinsu.

Jarabawar, wadda aka gudanar a dakin taro na Solomon Arase a hedikwatar hukumar, ta kunshi jami’ai kamar babban mataimakin sufeto janar (AIG), kwamishinoni biyu na ‘yan sanda (CPs), mataimakan kwamishina 11 (DCPs) da kuma mataimakan kwamishina 16 (ACPs) daga cikin mutum 17 da aka gayyata.

Shugaban PSC, tsohon babban mataimakin sufeto janar (DIG) Hashimu Argungu, ya bayyana cewa hukumar ta gabatar da wannan jarabawa ne domin tabbatar da cewa karin girma ya ta’allaka ne kan cancanta da bajinta.

Ya gargadi cewa duk jami’in da suka kasa tsallake jarabawar sau uku, za a tilasta masa yin ritaya daga aiki saboda rashin cancanta.

Ya ce duk da cewa an kawo jarabawar ne a karshe, hakan ci gaba ne da ake sa ran zai dawo da martabar rundunar ‘yan sanda ta Najeriya.

Argungu ya jaddada cewa yanayin tsaron duniya yanzu ya karkata ne kan kwarewa da iya aiki, don haka wajibi ne jami’ai su dage wajen shirya kansu don kalubalen aikin ‘yan sanda na zamani.

Ya kara da cewa hukumar za ta tabbatar da gudanar da cikakken bincike wajen kauce wa kuskuren karin girma ga jami’an da suka mutu ko suka yi ritaya.

Wannan jarabawar karin girma ta samu halartar tsohon alkalin kotun koli, Mai Shari’a Paul Adamu Galumje, da tsohuwar Mai Shari’a Christine Ladi Dabup, tsohon DIG Taiwo Lakanu, tsohon DIG Uba Bala Ringim da kuma Alhaji Abdulfatah Mohammed.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here